Matthew 15

1Sai wadansu Farisawa da malamai suka zo wurin Yesu daga Urushalima. Su ka ce, 2“Meyasa almajiranka suke karya al’adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.” 3Yesu ya amsa masu ya ce, “Kuma don me ku ke karya dokar Allah saboda al’adunku?

4Domin Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka; ‘Shi wanda ya yi muguwar magana ga mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lallai zai mutu. 5Amma kun ce, “Duk wanda ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, “Kowanne taimako da za ka samu daga gare ni yanzu baiko ne ga Allah,’” 6wannan mutum ba ya bukatar ya girmama mahaifinsa. Ta wannan hanya kun maida maganar Allah wofi saboda al’adunku.

7Ku munafukai, daidai ne Ishaya ya yi annabci akan ku da ya ce, 8“Wadannan mutane girmama ni da baki kawai suke yi, amma zukatansu nesa suke da ni. 9Suna mani sujada a banza, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin rukunansu.”

10Sai ya kira taron mutane zuwa gare shi ya ce masu, “Ku saurara ku fahimta, 11ba abin da ke shiga baki ke kazantar da mutum ba. Sai dai, abin da ke fitowa daga baki, wannan shi ya ke kazantar da mutum.”

12Sai al’majiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?” 13Yesu ya amsa ya ce, “Kowace shuka wadda ba Ubana na sama ya shuka ba za a tuge ta. 14Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami.”

15Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ka bayyana wannan misali a garemu,” 16Yesu ya ce, “Ku ma har yanzu ba ku da fahimta? 17Ko baku gani ba duk abin da ke shiga baki zuwa ciki ta haka yake fita zuwa salga?

18Amma abubuwan da ke fita daga baki suna fitowa ne daga zuciya. Su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. 19Domin daga zuciya mugayen tunani suke fitowa, kisan kai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, da zage-zage. 20Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum.”

21Sai Yesu ya tafi daga nan ya nufi yankin biranen Taya da Sidon. 22Sai wata mace Bakan’aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; ‘yata tana cikin bakar azaba da aljani.” 23Amma Yesu bai ce mata kome ba. Almajiransa suka zo suka roke shi, suna cewa, “Ka sallame ta, domin tana bin mu da ihu.”

24Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra’ila.” 25Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa, “Ubangiji ka taimake ni.” 26Ya amsa ya ce, “Ba daidai bane a dauki gurasar yara a jefa wa kananan karnuka.

27Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.” 28Sai Yesu ya amsa ya ce mata, “Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so.” ‘Yarta ta warke a lokacin.

29Yesu ya bar wurin ya tafi kusa da tekun Galili. Sai ya hau tudu ya zauna a can. 30Taro mai yawa suka zo gunsa. Suka kawo masa guragu, makafi, bebaye da nakasassun mutane da yawa, da wadansu marasa lafiya. Suka kawo su gaban Yesu, sai ya warkar da su. 31Don haka mutane da yawa suka yi mamaki a lokacin da suka ga bebaye suna magana, nakasassu sun warke, guragu suna tafiya, makafi suna gani. Sai suka daukaka Allah na Isra’ila.

32Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, “Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya.” 33Almajiran suka ce masa, “A ina zamu sami isasshiyar gurasa a wannan wuri da babu kowa har ta ishi babban taron nan.” 34Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da ‘yan kifi marasa yawa.” 35Sai Yesu ya umarci taron su zauna a kasa.

36Ya dauki gurasar nan bakwai da kifin, bayan ya yi godiya, ya kakkarya gurasar ya bada ita ga almajiran Sai almajiran suka ba taron. 37Jama’a duka suka ci suka koshi. Suka tattara gutsattsarin abincin da ya rage, kwando bakwai cike. 38Wadanda suka ci su dubu hudu ne maza, banda mata da yara. Sai Yesu ya sallami taron ya shiga cikin jirgin ruwa ya tafi yankin Magadan.

39

Copyright information for HauULB